A ci gaba da kokarin kwato yankunan da 'yan ta'adda na Da'esh suka mamaye,Sojojin Iraki sun kwato Gariruwan Samirra,Takrit tare da wasu aguwanni 4 a garin na Mosul
Wata majiyar tsaro daga birnin Bagdaza ta habarta cewa a safiyar yau wasu zutaran Sojojin Iraki sun tukanri Gari Mosul don taimakawa 'yan uwansu da nufin tsarkake Garin daga hanun kungiyar
Da'esh mai alaka da alka'ida.
Har ila yau Sojojin na Iraki sun hallaka wani babban komanda na Da'esh mai suna Abu Dujana Almagribi a Garin silahuddin .
A bangare guda kuma fiye da matasa dubu 30 ne wadanda suka fito daga kudancin Basra,arewacin Nainuwa, da kuma Najaf suka hade da sojojin kasar don yakar kungiyar Da'esh mai alaka da.kungiyar Alka'ida.